Kimanin kudi SEFA miliyon dubu har sau dubu ne ake biyar kasar Nijar bashi
Kungiyar nan mai yaki da karbar bashi da ruwa anan Nijar wato RNDD a takaice, tana shirye-shiryen gudanar da wani rangadi a sassa da dama na kasar nan domin fadakarda jama’a manufofin wannan kungiya da kuma ayukan da ta gudanar daga lokacin da aka kafa ta yau fiye da shekaru biyu da suka wuce kawo yanzu. Shugaban kungiyar ne Malam Ibrahim Yakuba ya bayyana haka lokacin da yake hira da jaridar Ra’yi anan birnin Yamai, inda yace tuni kungiyar tasu ta tsara jerin sunayen garuruwa da kuma wuraren da suke da mahimmanci ta fannin tattalin arziki ga kasar nan, wadanda ya ce tawagar ta su zata ziyarta a matsayin mataki na farko domin kara matso da jama’a zuwa ga fahimtar ayukan da wannan kungiyar ta ke yi.
Rangadin kamar yadda shugaban kungiyar yace, za’a kaddamar da shi ne ranar 18 ga wannan wata na Maris anan Yamai, inda kuma washe gari ranar 19 ga watan za su fita zuwa cikin sauran yankuna na kasar nan har tsawon mako daya. A ranar ta 19 ga watan Maris tawagar zata soma yada zango ne a garin Kure mai tazarar kilomita 50 daga Yamai, yankin dake da albarkatun gandun daji, wanda za ‘a iya samun kudaden shiga ta hanyar sa matukar dai gwamnati zata yi tattalen sa. Shugaban kungiyar ta RNDD ya cigaba da cewa bayan sun kammala da garin Kure sai kuma tawagwar ta wuce zuwa biranen Doso, Dogon Dutsi, Konni, Gidan Rumji,Tsibiri, Maradi har zuwa garin Damagaram.
A duk wadannan yankuna kamar yadda Ibrahim Yakuba yace, za su wayarda kawunan jama’a ne mahimmanci irin ayukan da kungiyar ta su ke yi domin kawar da talauci a cikin al’ummar wannan kasa. Domin irin mahimmanci da wannan kungiya ta RNDD ke da shi wannan yasa baki daga kasashen turai aminan kungiyar, zasu kasance tare da tawagar a duk inda zata ziyarta, domin su gane ma idanuwan su irin ayukan da kungiyar ke aiwatarwa, da kuma sanin irin hali na talauci da al’ummar wannan kasa ke rayuwa a cikin sa.
Abin tuni anan shine ,wannan kungiya mai gwagwarmaya da bashi da ruwa wanda kasashen duniya masu hannu da shuni ke baiwa kasashe matalauta, ta taba shirya wani rahoto mai dauke da koke-koken jama’ar wannan kasa, a wani kundi tare da sa hannun yan kasar ta Nijar akalla dubu bakwai, kana ta mikawa wakilin bankin duniya dake nan Nijar domin ganin cewa an yafewa kasar irin basusukan da bankin na duniya da kuma asusun bayar da lamuni na bankin duniyar FMI ke biyar wannan kasa.
Irin basusukan da wadannan kungiyoyi na duniya ke biyar kasar Nijar kimanin shekaru 25 da suka gabata, duka duka SEFA miliyon dubu 27 ne, to amma a yanzu irin bashin da ake biyar wannan kasa ya kai SEFA miliyon dubu har sau dubu, kuma a kowace rana karuwa ne ya ke ba raguwa ba duk da cewa an yafewa kasar bashin SEFA miliyon dubu dari shida a cikin shekarar da ta wuce. Daga karshe dai shugaban wannan kungiya ta RNDD, yace lalle idan har ba gwagwarmaya aka yi ba domin yafewa Nijar dimbin bashin dake kanta ba, to lalle kuwa zancen samun cigaba ko kuma kawar da talauci abu ne mai wuya matuka a kasar Nijar. A ranar 26 ga wannan wata ne dai kungiyar zata kammala rangadin nata da zata kaddamar ranar ta 18 ga wannan wata na Maris.
Abdulkarim Ibrahim