kungiyoyin gari da makamantansu, masu tahiyar da ayukka a cikin sassa da dama na bunkasa, ko da yake an san da zamansu, mahi yawancinsu ba su da takardar aihuwa kan gaskiya. Gwamnati na yarda da su a sabilin yarjejeniyar hulda da ke akwai tare da masu hannu da shuni. -ar sa in sa da ke hada su da gwamnati ba ta huce kara takarya ba. Kuma tana da alaka da tattalin daji, kamar a misali kasuwar itace.
Amma ga wannan tsarin da za a shiga na sassauta iko, rigimar za ta girma tun da magabatan da za a dauka, za su so su yi amfani da duk wasu hanyoyin samun kudi na tahiyar da ayukkan karkara. Hakan zai sa su amshe wasu ayukka da tun a zal kungiyoyin ke zartarwa.
Wata kwamin za ta bar wata kungiya da ba a sani ba kan shari’a da dokar kasa ta tahiyar da dumbun kudin da ake samu ga kasuwancin giginya, kasuwar itace, rarraba ruwa ko tabakuna. Wannan misali ne kawai na fannin tattalin arziki. Lalle zai yi wuya don sabbin kwamin za su so su amshi wannan aikin har ma su kara hanyoyin shigar kudi.
Za a ga kamar akwai hulda ko a samu shan ban-ban. Ana kiransu da sunaye kamar haka : bada amurni, kwangila, tahiyar da aiki cikin walwala … ko kuma ya dace a ce sabbin ma’aikatan da za a kawo su samu a gabansu kungiyoyin da ake sani kan shari’a masu iya kare hakkinsu.
Wadannan hanyoyin ba su samuwa har sai an samu kasancewa sananna, wato karkashin duk wata kungiya mai zaman kanta. Wannan kasancewa kan gaskiya da shari’ar kasa zai sa dole a dama da kungiyoyin ci- gaban karkarinne a cikin karkara ko kuma lokacin da aka sassauta iko. Amincewa da yin takardun aihuwa ga wannan kungoyoyi, wani guri ne da ya kamata a cimma.
Gurori
- sanin mahimmancin takardar aihuwar kungiyoyi ;
- sanin hanyoyin da ya kamata abi don yin takarda ;
- sanin ire-iren takardun da ya kamata a hada don samun takardar aihuwa.
Kashi na farko : Mahimmancin sanin kungiya kan dokar kasa
Mai waye kai zai yi amfani da yin tambayoyi don hiddo matsaloli da cikas da ake samu idan ba a san da zaman kungiya ba ga shari’a, sai a fassara yadda ake yi don sanin zaman kungiya.
Alal misali :
- bayan mutanen da ke shugabacinku a cikin kungiya wanda ku ka zaba, akwai masu ba ku umurni ko su shiga cikin harakar kungiyarku, kamar : sarki, masu girma kumandan…?
- a matsayinku na kungiya, har kun taba bin wani wurin shari’a da kuka ga ya kamata don ya ci kudinku ko ya maku sata… ?
- a matsayinku na kungiya, ku taba yarjejeniya da wasu kungiyoyi ko ma’aikatu bayan wanda suka dafa maku kuka ga hanya don zartar da tsarin ayukkanku a sashen kiyon lahiya, noma, kiwo, bashi, gine-gine…?
- kuna da hulda da hukuma bayan horojen da ke dafa maku ?
- idan horoje ta zo gare ku a cikin karkara tana bi gare ku ko kuma idan kun je a birni , akwai wata shaida da ke sa a gane ko daga wace kungiya kuka hito ?
- harkun taba sa hannu bisa wata kwangila da ma’aikatun gwamnati ?
- kuna iya samun bashi daga wani banki bayan masu dafa maku ?
Ku tambayi mahalarta har in sun san wasu kungiyoyi wadan da ba su cikin wannan halin ? Ku tambaye su dalili, kuma a cikin hirar su gano da cewa lalle rashi ba a san kungiyarsu ba ya kawo wannan matsalar.
A Tambayi mahalarta su hiddo mahimmancin sanin kungiya da takardar aihuwa. A rubuta a babban allo tare da yin kari da rubutu na 9.
karin Bayani na 9 : Amfani sanin zaman kungiya
- sanin kungiya na sa ta zamna kan shari’a daidai da sauran ;
- hakan zai ba kungiyar damar bin wani wurin shari’a ;
- samun arziki na kanta ;
- iya gamewa ko yin majalissa da duk sauran kungiyoyi masu hangen guri guda ;
- yin yarjejeniya da sauran abukkan hulda ;
- buda asusu ko samun bashi ;
kashi na 2 : Yadda ake yi a kafa kungiya
Mai waye kai zai fassara ma mahalarta da cewa dokar kasa ta amince ga yan kasa su yi tsarinsu cikin walwala don gudanar da ayukka da dama. Dangance da gurorin da ake so a cimma, ana samun kungiyoyi masu neman riba da wadanda ba kudi suke nema ba.
A tambayi mahalarta da su zana wasu kampanoni da wani gungun jama’a ya kera na tattalin arziki, siyasa, raya gari. A kara tambayar su don bada abinda kowace kungiya ke yi da abin da take nema don numa cewar shiga cikin wani rukunin kungiyoyi ya danganta da gurin da ake son cimma. Don kare wani hakkin da ba na samun riba ba, an bada uzirin a yi kungiya ko kungiya mai zaman kanta (ONG), idan gungu ne mai son karfafa kasuwancinta a nan ana yin “GIE” (gungu mai neman riba ko koperatib), ga masu kudi masu son su buda kampani kamar na suhuri, sai su buda kampani mai nauyi a kayyade.
A takaice mahawarar ta hiddo cewar abu na farko da ya kamata don a san da zaman kungiya ya zan tan kafe tare da cewar lalle mutanen sun hiddo matsalolin da suke son su shawo kansu tare :
- Daga dalilin kafa kungiyar zuwa gurorin da ta sa gaba (kare hakin dan- adam, karfafa yancin mata, kare yanayi samun tsabtaccin ruwan sha…) ;
- Fassara irin kungiyar da ta dace don cimma gurorin ;
- Fassara irin tsarin da za a yi don bayyana gurorin yadda ya kamata ;
- Yadda za a yi don tahiyar da aiki ….
Ya kamata su hidda kundin tsarin kungiya da za’a amince da shi ga babban taro. Wannan babban taron zai nada wasu mambobi na rikon kwarya da za su tahiyar da kungiyar. Sanayen wadanda suka halarci taro da har ma takardar shaidar taro ko takardar rahoto.
A takaice tare da hiddo hanyoyin kafa kungiya : Wata matsala da yan karkara suka gano, wata niyyar samun matakkai ta hanyar hada karhinsu, irin kungiyar da suka zaba, rubuta kundin tsarin gudanar da kungiyar, taruwa ta masamman, kafa buro, rubuta sunayen mahalarta da yin takardar rahoto.
karin Bayani na 10 : Kundin tsarin tahiyar da kungiya tare da ka’idodi
Kundi wani ne da masu kafa kungiyar za su tsara. Yana fassarar gurorin kungiyar, tsarinta da tahiyar da aiki.
A mahi yawancin halaye, ga yadda ake tsaida kundin ko da yake dokokin sun bambanta daga wata kungiya zuwa wata.
Kai na 1 : sunan kungiya, gurorinta, wa’adinta, inda take zaune.
Kai na 2 : yadda ake shiga kungiyar, yanci da nauyin da ya rataya ga mambobi, hidda mutum ko hukumce-hukumce da suka dace.
Kai na 3 : yadda aka kalkasa kungiyar da tsarinta, za a shinkida dokokin da ke kayyade abin da ta kumsa ;
Kai na 4 : hanyoyin samun kudi ga kungiyar, inda suka hito (kudin yadda take kashe su, shiga wani gungu ko majalissa, roshe kungiyar, wasu matakkai na sake tilawar dokokin.
karin Bayani na 11 : Ka’idodin tahiyar da kungiya
Yana nuna tsarin tahiyar da kungiya kamar nauyin da ya rataya ga kowane mamba, yadda sauran gabobi ke aiki (na kasa da kungiya, yadda ake daukar matakkai.
A yawancin halaye ga abin da ke cikin wannan kundin :
* yadda ake fita ko shiga cikin kungiya ; * tsari da mahimmancin taro ga kowane hawa ; * abin da kungiya ta kumsa, zabe, bada nauyi ga mambobi daban-daban .
Kashi na 3 : Kundin sanin zaman kungiya
Tahiyar da aiki
A tambayi mahalarta har in kungiyar da aka kafa kamar yadda aka fada a baya na iya tahiyar da ayukkanta cikin walwala, idan ba haka ba sai a ba da dalili ?
A nan za a kawo mahalarta su gane da cewar babu wata hukuma da ta san da ita a yanzu illa kawai mambobinta.
Ta kan yiyu ka’idodin da suka tsaida sun saba ma dokar kasa don haka sai an yi bincike kahin hukuma ta rubuta wannan kungiyar ga saninta.
A tambayi mahalarta :
- su bada ire-iren takardun da suka dace don tambayar takardar aihuwa;
- su yi dan bayani bisa kowace takarda ;
- ina ne ake kai takardun ?
Basu bayanin cewa idan aka aje takardun, za a rubuta su cikin kundin ma’aikatun gwamnati da za su ba kungiyar wata takarda mai ba ta damar gudanar da ayukkanta cikin walwala, samun takardar aihuwar zai hito a gaba daga wurin ministan cikin gida da ma’alkatar karkara za ta daukar makamancin kundin (takarda) don sanar da shi ga radiyon kasa kuma nauyin na bisa kan kungiyar.
karin Bayani na 12 : Registan kungiyar
Wata shaida ce da ke nuna cewa lalle kungiyar an rubuta ta cikin makamantanta a can wurin ma’aikatar (kowace irin kungiya da nata wuri da ta dace.
Tambayar rubutu kundi zai hito ga shugaban kungiyar ko duk wani mutum na cikin kungiyar da za a ba dama, kundi na dauke da takardu iri 2 :
- takardar shaida taron kafa kungiya ;
- takardar tambayar rubutu kundi (wasika ce zuwa ga ma’aikatar da ke karbar kundaye daga kungiya mai tambaya cikin regista ;
- dokokin kungiya (a dubi rubutu na 11) ;
- Ka’idodin tahiyar da kungiya (rubutu na 11 ;
- takardar fasali (tsarin ayukka) ana tambayar ta ga irin kungiyoyi masu zaman kansu (ONG) ;
- kudin rubutu : ana biyan jikka 5 (5.000 F) wurin aje kundi.
Bayan an aje kundi wato an rubuta, sai hukumar ta bada wata takarda mai nuna an rubuta kundin kuma mai ba kungiyar damar gudanar da ayukkanta cikin walwala har wani lokaci.
Takardar aihuwa
Wata takarda ce mai mutumta kungiya. Kundin tambayar da aka aje na sanin kungiya shi ne ke sa kuma a samu takardar aihuwa ta hanyar tambaya. Takardar na hitowa daga ministan cikin gida, ma’aikatar karkara da sanar ga radiyon kasa a bisa nauyin kungiya.
karin Bayani na 13 : Takardar Shaidar Taron Kafa kungiya
Takardar rahoton taro na masamman
An taru a …………………………… ranar ………………………… mambobi da za a hadawa da wannan takardar (sunayensu) sun kafa kungiya kamar yadda kudiri mai lamba 96- 067 na 9 ga watan nobamba 1996 da kudirin aikatawa mai lamba 96- 430\PRN\MAG\EL na 9 ga watan nobamba 1996.
A dangace da haka, taron ya tsaida matakkai kamar haka :
Matakin farko
Dokoki da ka’idodin tahiyar da aiki sun samu karbuwa ga duk mahalarta ;
Mataki na biyu : wuri
Wurin zaman kungiyar shine …
Akwatin takarda….
Mataki na ukku
Lokacin wannan taron, mambobin da aka zaba (na rikon kwarya su ne : Makami
Suna da sunan uba, shekaru, aiki, wurin zama
- shugaba
- mataimakinshi
- maga-takarda
- ma’aji
- mamba
An sa masu bincike
Suna da sunan uba, shekaru, aiki, wurin zama
Bayan an gama taro shugaba ya sallami kowa
An yi shi a ……………………..
Maga- takardan da ya rubuta
Malam …………………….
Fasalin aikin kungiya
Gurin kungiyarmu shine yaki da rashin abinci ga mambobin kungiyar. Ga yadda ayukkanmu za su kasance : lokacin damana (yuni zuwa Ogusta )
Kungiyamu za ta saida ma mambobinta cimaka kai tsaye ga farashi mai rahusa. Duk mambobin na iya saye, haka kuma cikin wannan lokacin idan mambobin kungiyar na cikin matsi na rishin cimaka za a iya basu bashin abinci don kar su bar gari da gonakinsu su je nema idan aka hidda albarkatun gona sai su maida (oktoba zuwa janairu don a aje. Haka kuma kudin da aka samu lokacin da aka saida cimaka, za a sake sayen cimaka da su. Magabatan da aka sa za su lura don ganin ayukkan na tahiya daidai.
Kungiyar tamu na hulda da kungiyoyi makwabta don kyautata ayukkanmu da kyautata rayuwar mambobinmu gaba dayan su.