Raya karkara a Jahar Maradi

Raya karkara a Jahar Maradi

Yankuna da dama ne a nan kasar Nijar ke cin moriyar ayukan raya kasa da kuma cigaban jama’a wadanda kungiyoyin bayarda agaji na kasa da kasa da kuma projet ke gudanarwa kowace shekara ta Allah.Mafi yawa daga cikin irin ayukan da wadannan kungiyoyi ke gudanarwa, mazauna yankunan karkara ne suka fi amfana dasu, ayukan da suka hada da bunkasa ilimi, samarda ruwan sha da kuma bunkasa ayukan noma .

ahar Maradi tana daya daga cikin jahohin da suke amfana da ayukan da wani Projet mai suna PDLM yake gudanar yau shekaru da dama.Shi dai wannan Projet wanda yafi mayarda hankali game da ayukan cigaban yankunan karkara, yana taimakawa Al’umar ta jahar Maradi ne a fannonin da suka kumshi samarda ingantaccen irin shukawa ga manoma,gina riwoji domin samarda ruwan sha mai tsaba,da gina makarantu domin yaki da jahilci da dai sauransu ….

Projet PDLM yana samun kudaden tafiyar da ayukan sane daga kasar suwiziland, kasar dake tallafawa Nijar ta fannoni da dama na cigaban mazauna yankunan karkara tun shekara 1962.Zancin da ake yanzu haka,gundumomi kamarsu Shadakwari, Sabon mashi, Saye Sabuwa da kuma Tsibirin Maradi, sune ke morewa ayukan da Projen keyi yau shekaru tara kenan. Akalla dai makarantun yaki da jahilci guda 220 ne Projet PDLM ya buda a cikin wadannan gundumomi, makarantun da suka yaye dalibai kimanin dubu biyar da dari takwas(5800)wadanda suka kware ta fannin iya karatu da rubutu a cikin harsunan Hausa da Turanci, inda kuma yake da niyyar habaka ayukan sa zuwa wadansu yankuna na jahar ta Maradi anan gaba kadan.

Malam Yahaya Mahamadu babban jami’in dake kula da wannan Projet a jahar ta Maradi, ya shaida mana cewa a fannin yaki da jahilci kawai, kimanin kudi SEFA miliyon 25 zuwa 60 ne suke kashewa ko wace shekara, inda kuma yaci gaba da cewa akwai wadansu kudaden da ake warewa sauran fannoni na raya karkara. A wannan zamani kuwa na demokradiya, PDLM ya hada guiwa da wata kungiya mai suna DEMOCRATIE 2000 domin bayar da horo ga zababbin yan majalisar mashawarta wato Conseillers da kuma wani horo na daban ga jama’ar wadannan yankunan game da hakkokin bil’adama.Al’umar jahar Maradi baki daya suna matukar shawar wadannan ayukan da Projen ke gudanarwa, musamman ma sarakunan gargajiya dake taka mahimmiyar rawa a cikin wannan tsari na kyautata rayuwar mazauna yankuna karkara.

Salisu Isa daga Maradi